
‘Yansanda sun fara aiwatar da dokar hana amfani da gilashin mota mai duhu ba tare da izini ba daga ranar Alhamis, 2 ga watan Oktoba.
Sanarwar hakan ta fito ne daga hedkwatar rundunar ‘yansanda shiyya ta 7 da ke Abuja, inda ta ce hakan umurnin babban Sufeto Janar Olukayode Egbetokun ne.
A sanarwar mai dauke da sa hannun jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar shiyya ta 7, ASP Halima Mohammed, ta buƙaci masu amfani da motoci musamman a birnin Abuja da jihar Neja su tabbatar da suna da sahihan takardun shaidar izinin amfanin da gilas mai duhu.
“Wa’adin da aka ɗibar wa masu motoci su nemi izinin amfani da gilashi mai duhu ko kuma su sabunta takardunsu ya ƙare, saboda haka daga yanzu dole ne duk wani mai amfani da irin wannan gilashi ya nuna shaidar izinin da aka bashi ko kuma ya fuskanci hukunci”.
Sanarwar ta yi gargadin cewa amfani da gilashi mai duhu ba tare da izini ba laifi ne, kuma jami’ai za su riƙa yawo don kama wadanda suka saɓa dokar, kuma duk wanda aka kama za a ƙwace motarsa ko kuma ya gurfana gaban kotu.