Majalisar Dattijai ta ce kar ‘yan Najeriya su tsammaci amincewarta da kasafin kudin nan da watan Janairu.
Shugaban Kwamitin Yada Labarai Da Hulda da Jama’a na Majalisar, Sanata Yemi Adaramodu (APC, Ekiti South)ne ya shaida wa manema a ranar Lahadi a Abuja.
“Sai ranar 7 ga watan Janairu ma’aikatun gwamnati da hukumomi da sauran sassa na gwamnati za su fara kare kasafin kudinsu a gaban zauren majalisar”. Inji shi.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudin na naira tiriliyan 49.7 ga zaman hadin gwiwa Majalisar Tarayya a ranar 18 ga Disamba.
Ya kuma bukaci ‘yan majalisar da su gaggauta amincewa da kudirin kasafin kudin na shekarar 2025.
Kakakin Majalisar Dattijai ya kuma ce, kwamitocin hadin gwiwa na Majalisar Wakilai da na Dattijai kan Kasafi za su gabatar da rahoton karshe na kasafin a ranar 31 ga Janairu.
Tuni dai kudirin kasafin kudin ya riga ya wuce karatu na biyu a majalisun biyu na Majalisar Tarayya (Majalisar Dattijai da Majalisar Wakilai).