Majalisar dokokin Kano ta tabbatar da Rasuwar mambobinta biyu da suka rasu Sa a tsakanin junansu
‘Yan majalisar dukkaninsu sun rasu ne a yammacin Laraba.
Mai Magana da Yawun Majalisar Kamaluddeen Sani Shawai ne ya tabbatar da rasuwar su , a hirarsa da wakiliyar Premier Radio.
“Marigayi Aminu Sa’adu Ungogo, ɗan majalisa mai wakiltar Mazabar Ungogo kuma Shugaban Kwamitin Kasafi ne ya Fara rasuwa.
Daga bisani Dan majalisar Mai wakiltar kwaryar birni wato Municipal Abdullah Sarki Daneji shima ya rasu”. In ji shi
Shawai a madadin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Honorabul Jibril Ismail Falgore, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan ‘yan majalisun da kuma al’ummar kananan hukumomin biyu tare da sauran abokan aikinsu.
An yi jana’izar Dan majalisar Ugoggo marigayi Aminu sa’adu, ana kuma inda sa ran yin jana’izar Dan majalisar karamar hukumar Birni marigayi Abdullahi Sarki Daneji yau Alhamis, a kofar kudu wato fadar sarkin Kano
