Sun kakkarya tebura da latata sauran kayyakin aiki a lokacin fadan a tsakaninsu a yayin tantance ministocin da shugaban kasar ya aike musu.
‘Yan majalisar sun danbace ne a lokacin da hatsniya ta barke a tsakaninsu a lokacin da suke tantance wasu mutane uku da domin ba su mukamin ministocin da shugaban kasar John Mahama ya aike musu.
Hatsaniyar ta faru ne a yayin zaman tantancewar a ranar Alhamis da daddare.
Babban abin da ya haddasa hatsaniyar da ta kai doke-doke shine tantance ministan Sadarwa Mista Samuel Nattey George wanda ya dauki tsawo sa’oi biyar.
Mista George a yayin tantancewar ya tsaya kan bakansa na wasu kalamai da yayi na cewa gwamnatin ‘yan adawa da suka kayar a zabe ta ‘yan cin hanci da rashewa ce wanda hakan ya fusata su.
“Ni mutum ne mai tsari, ba na guduwa kan duk abin da yi imani da shi, don haka ina kan bakata kan abubuwan da na faɗa kan tsohon shugaban ƙasa da kuma sauran jami’an gwamnati.” in ji Samuel George.
hakan ta kai ga dakatar da tantance sauran mutanen biyu daga ‘yan adawa ta kma kai ga hatsaniyar da ta haifar da dambe da kuma barnata kayyyakin aiki.da suka haɗa da kujeru da kuma makurufo dasuransu.
Shugaban bangaren gwamnati a majalisar Mahama Ayarigah ya nuna takaicinsa kan hatsaniyar da ta faru a majalisar.
BBC ta rawaito cewa mutane da dama sun yi tir da ‘yan majalisar kan abin da ya faru, kasancewar wannan ba shi ne na fari ba.
A watan Janairun 2021, ‘yan majalisar ƙasar sun bai yi irin wannan damben a lokacin zanen kakakin majalisar, wanda hakan ta kai ga tura sojoji da ‘yan sanda domin shiga tsakani.