
Ƙungiyoyin masu fafutuka a Madagascar sun kira gagarumin zanga-zangar adawa da gwamnati a babban birnin ƙasar, domin neman shugaba Andry Rajoelina ya yi murabus.
Zanga-zangar ta fara ne tun ranar 25 ga Satumba sakamakon yawan yanke wutar lantarki da ruwan sha, amma daga bisani ta rikide zuwa neman kawo ƙarshen mulkin shugaban mai shekaru 51 wanda yake kan madafun iko tun 2018.
A ranar 29 ga Satumba a yunkurin kwantar da hankulan masu zanga-zanga, Rajoelina ya kori dukan ministocinsa tare da alƙawarin naɗa sabon firaminista.
’Yan wasan kwaikwayo da masu tasiri a kafafen sada zumunta da ƙungiyoyin ƙwadago da na farar hula sun bayyana goyon bayansu ga zanga-zangar.
A yau da safe gidan rediyon Faransa RFI ya ruwaito cewa masu zanga-zangar sun naɗa mutum takwas a matsayin jakadunsu, domin su wakilci muryar gungun masu adawa da gwamnati.
Sai dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aƙalla mutum 22 ne suka mutu yayin da sama da 100 suka jikkata a rikicin da ta ɓarke a lokacin zanga-zangar da aka gudanar a makon da ya gabata, abin da hukumomin Madagascar suka musanta, suna mai cewa labaran “jita-jita da bayanan karya” ne.