Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da ake tsaka da aiki da yarjejniyar tsagaita wuta da aka kulla ta kuma soma aiki a ranar Lahadi .
Falasɗinawa fiye da 21 ne suka jikkata yayin da wasu ‘yan kama-wuri-zauna na Isra’ila suka kai hari a garuruwansu.
Garuruwan da ‘yan isara’ilan suka kai hari sune Jinsafut da Al-Funduq kusa da birnin Qalqilya a arewacin Gabar Yamma da Kogin Jordan.
Maharan sun yiwa Falasdinawan duka tare da fesa musu iskar gas mai sa hawaye daga dakarun Isra’ila.
Ƙungiyar Palestinian Red Crescent Society ta sanar da cewa tawagar likitocinta ta bayar da magunguna ga mutanen da suka jikkata.
Harin na zuwa ne a lokacin da ake aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, wanda kasashen Qatar da Masar da kuma Amurka suka shiga tsakani wajen kulla ta ranar Lahadin da ta gabata.
