
Wasu da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari kan tawagar tsohon Ministan Shari’a kuma tsohon Antoni Janar na Tarayya Abubakar Malami (SAN) a yayin da yake ziyarar jaje a Birnin Kebbi, babban birnin jihar Kebbi.
Malami, wanda a baya babban jigo ne a jam’iyyar APC, da ya sauya sheka zuwa ADC, ya zama jagora a jihar, ya tsallake rijiya da baya yayin da shi da tawagarsa suka yi arangama da matasan a safiyar Litinin.
Shaidun a lamarin da ya faru sun bayyana cewa, an lalata akalla motoci 10 wasu daga cikin magoya bayan tsohon ministan sun samu raunuka, sakamakon jifan duwatsu da kuma amfani da makamai da masu harin suka yi.
Da yake magana da manema labarai bayan harin, Malami ya bayyana cewa, ba siyasa ce ta kai shi jihar ba.
“Na je Birnin Kebbi ne domin jajantawa iyalan wasu fitattun mutane da suka rasu a lokacin da bana jihar, amma harkar siyasa bace.” In ji shi
Jam’iyyar APC reshen jihar Kebbi a wata sanarwa daga Sakataren Yaɗa Labarai na APC a Kebbi, Isa Assalafy, ta ce bata da hannu a cikin harin, tana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici da rashin dacewa.
APC a jihar ta zargi jami’an tsaro da ke cikin tawagar Malami da harbin bindiga, lamarin da ta ce shi ya haddasa rikicin.