
‘Yanbindiga sun sace kansiloli biyu da limamin wani masallaci a garin Tsauni da ke birnin Gusau na jihar Zamfara.
Kansilolin na mazabun Gidan Goga da Tsibiri a Karamar Hukumar Maradun, an sace su ne da misalin karfe 8 na daren ranar Laraba a kusa da ofishin ‘yan sanda da ke yankin jim kadan bayan kammala sallar Magariba.
Shugaban karamar hukumar Maradun Sanusi Gama Giwa ne ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce dukkansu ‘yan mazabarsa ne.
“Mutanen na hutawa ne a wurin wani mai shayi, lokacin da ‘yanbindigar suka far musu, tare da kwace wayoyin ‘yansandan da ke wurin da awon gaba da mutum 6, amma daga bisani sun sako uku sai dai sun tafi da Limami da kuma kansilolin biyu.” In ji shi.
Rahotanni sun ce sun zo neman wani mutumin karamar hukumar Kaura, amma da ba su gan shi ba su kai awon gaba da mutanen da ke wurin mai shayin.
Kawo yanzu dai babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro kan lamarin.