Maharan da ake zargin ’yan bindigar Lakurawa ne sun kai hari wani shagon canjin kuɗi a kauyen Durusar Gawo da ke Ƙaramar Hukumar Gudu ta jihar Sakkwato, inda suka kashe mutum biyu sannan suka raunata guda.
Wani ganau ya shaida wa jaridar Aminiya cewa maharan sun shiga yankin ne da ƙarfe 2:50 na rana, kuma kai tsaye suka nufi ɓangaren masu canjin kuɗi a kasuwar garin.
A cewar majiyar, ’yan bindigar da suka kai harin kusan su 11 ne, suka fara harbe-harbe kan ’yan kasuwa da mazauna yankin, inda suka kashe manyan ’yan kasuwa biyu, Alhaji Ummaru da Alhaji Sani, waɗanda aka sani da sana’ar canjin kuɗi a yankin.
Mazauna yankin sun roƙi Gwamnatin Jihar Sakkwato da hukumomin tsaro da su gaggauta kai musu dauki.
