Al’ummar garin sun ce ‘yanta’addar sun kai wani hari a kasuwar garin inda suka tafi da gwammon mutane tare da jikkata wasu tana tsaka da ci.
Mazauna yankin sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne a ranar Alhamis.
Sai dai har kawo yanzu rundunar ‘yansandan jihar ta Zamfara ba ta ce komai kan harin.
Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da Bello Turji ya yi barazanar kai hare-hare kan al’umma bayan kame wani na hannun damansa.
A makon da ya gabata ne sojoji suka kama makusancin nasa, al’amarin da ya ce ya fusata shi kuma zai dauki fansa.