Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai hari kauyen Zurum Mahauta Gidan Malam Sallau a garin Lakwaya dake karamar hukumar Gwarzo.
Maharan sun kai hari ne da misalin karfe 12 na daren Lahadi, inda ake hashen sun sace mutanen da ba a tantance adadinsu ba.
Wata majiya da ta nemi a sakaya sunan ta daga garin, ta tabbatar wa da Premeir Radio faruwar lamarin, ta kuma ce Sojoji sun kai dauki, inda suka bi sawun barayin
“Barayin sun tsallako ne daga jihar Katsina, kuma suna kammala ta’addancinsu suka dauki hanya suka koma.” In ji mutanen garin.
Kawo yanzu, babu labarin ko jami’an tsaro sun cimma barayin dake kan Babura.
Gwamnatin jihar na kokarin dakile hare-haren ‘yan bindigar a kananan hukumomin Kano dake kan iyaka da Jihar Katsina.
