
Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari a sakatariyar Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe, da sanyin safiyar Juma’a.
Rahotanni sun ce yayin harin, maharan sun harbi wani jami’in ɗan sanda da ke gadin sakatariyar suka ji masa rauni ƙafa.
Lamarin dai ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na dare, inda maharan suka buɗe wuta.
Shugaban ƙungiyar NUJ reshen jihar, Rajab Ismail Mohammed, ya bayyana harin a matsayin abin tayar da hankali da kuma babbar barazana ga lafiyar ’yan jarida a jihar.
Ya yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta gudanar da bincike kan lamarin tare da gurfanar da maharan a gaban kotu.
Ƙungiyar ta kuma yi kira ga hukumomi da su ƙara ƙaimi wajen samar da tsaro ga ƙwararrun kafafen yaɗa labarai da cibiyoyin yaɗa labarai a faɗin jihar, inda ta jaddada cewa irin waɗannan hare-hare na iya kawo cikas ga ’yancin ’yan jarida da kuma samun damar yin amfani da bayanan jama’a.
Ƙungiyar ta jaddada cewa kare ‘yan jarida na da matuƙar muhimmanci ga ci gaban dimokuraɗiyya da riƙon amanar jama’a.
Yanzu haka dai dan sandan da aka harba na can a sashin gaggawa na asibitin ’yan sanda da ke Damaturu.
Rahotanni sun ce hukumomin ’yan sanda sun fara gudanar da bincike domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin.