Kwamishinan harkokin tsaro na jihar, Dr. Nasir Mu’azu, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar yau Asabar.
Sanarwar ta ce dakarun Community Watch Corps sun yi nasarar fatattakar maharan, sai dai daga baya ƴan taʼaddar sun musu kwanton ɓauna yayin da su ke jigilar waɗanda suka jikkata zuwa asibiti, inda suka ƙone motar jamiʼan.
Gwamnati ta yi ta’aziyya ga iyalan da suka rasa ’yan uwansu tare da fatan samun sauƙi ga waɗanda suka jikkata, tana mai jaddada cewa za ta ci gaba da aiki tare da hukumomin tsaro don kawar da barazanar ’yan ta’adda.
