
Gwamnatin tarayya ta rufe wuraren sayar da magunguna sama da dubu arba’in a fadin Najeriya cikin watanni 15
Ta yi haka ne a wani bangare na kokarin tsaftace fannin magunguna da kuma tabbatar da ka’idojin da aka shimfida.
Magatakarda na Hukumar Kula da harkokin Magunguna ta Najeriya PCN, Pharmacist Ibrahim Baba Shehu ne ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin wani taron bita na kwanaki biyu da hukumar ta shirya tare da hadin gwiwar Hukumar Kebantaciyar Cibiyar Sayar Da Magunguna Ta Kanawa.
Pharm Ibrahim Baba-Shehu ya jaddada cewa, PCN ta shirya taron ne ga masu gudanar da sana’a a kebantacciyar cibiyar bisa tsarin doka dake Dangwauro a jihar Kano da nufin ilmantar da masu sayar da magunguna yadda ya kamata da kuma bin ka’ida.
A nasa jawabin Shugaban hukumar, Alhaji Hussaini Labaran Zakari, ya yabawa shirin, inda ya bayyana shi a matsayin wani muhimmin mataki na inganta iya aiki, da kare lafiyar al’umma, da inganta sana’a a fannin.
Hukumar ta ce, an yi nasarar Kwace jabun magunguna da marasa Inganci da kuma miyagun kwayoyi na Kudi Sama da Billiyan 1 a Jihar Kano cikin Lokacin da aka ambata.