
Daga Safina Abdullahi Hassan
A cewar masana kiwon lafiya, sankarar mama na daga cikin manyan cututtukan da ke kashe mata da yawa a duniya, musamman a kasashe masu tasowa.
Rashin samun kulawar likita da kuma karancin wayar da kai, na kara tabarbarewar lamarin, a cewar hukumomi.
Don haka kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomin gwamnati kan gudanar da gwaje-gwajen lafiya kyauta, da tarukan ilmantarwa domin ankarar da jama’a da kuma bukatar mata su rika duba kansu lokaci zuwa lokaci.
Dakta Aliyu Sani Kabo, kwararren likita a Asibitin Koyarawa na Malam Aminu Kano, a hirarsa da wakiliyarmu, ya yi karin haske game da cutar.
”Ba manyan mata ne kadai ke iya kamuwa da cutar ba, ‘yan mata ma kamuwa da ita.
“Akwai bukatar mutane musamman mata, su dinga zuwa asibiti da zarar sun samu sauyi a jikinsu.
”Cutar Kansa ana iya gadonta, a wasu lokutar kuma mutum na iya kamuwa da ita ne ba ta gado ba”. In ji shi.
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ware watan Oktoba a matsayin watan wayar da kan jama’a kan cutar sankarar mama a duniya.
Taken bikin na bana shine, kowace rayuwa da labarinta, kuma kowace tafiya tana da muhimmanci.