
Ganawar da gwamnatin tarayya da shugabannin ƙungiyar ma’aikatan Mai da Gas ta ƙasa, NUPENG, a Abuja ya ƙare ba tare da cimma matsaya ba, duk da tsawon sa’o’i bakwai na tattaunawa.
Ministan Kwadago da Nagartar Aiki, Muhammad Maigari Dingyadi, ne ya jagoranci ganawar wadda aka gudanar domin warware matsalolin da suka janyo yajin aikin da NUPENG ta fara a ranar Litinin da ta gabata.
Rahotanni sun ce kamfanin mai na Dangote ya janye daga dakatarwar da ya yiwa ma’aikatansa daga shiga yajin aikin NUPENG, wanda hakan ya ba da sabon fata a shirin sulhu.
A ganawar, an samu halartar manyan wakilai daga bangarorin daban-daban ciki har da Sayyu Dantata da Jibrin Otunba daga kamfanin Dangote, Dr. Nuhu Toro, Shehu Muhammad, Onyeka Chris da Opaluwa Simon daga ƙungiyoyin kwadago na NLC da TUC tare da shugaban NUPENG, Williams Akporeha.
NUPENG ta bayyana yajin aikin ne sakamakon shirin matatar man Dangote na shigo da tankokin dakon mai masu amfani da iskar gas na CNG guda 4,000, domin kai mai ga masu sayarwa kai tsaye, matakin da kungiyar ta ce zai rage ayyukan mambobinta.
Matatar ta fuskanci kalubale a kasuwar mai ta Najeriya, inda wasu yan kasuwa ke shigowa da tataccen mai daga ƙasashen waje maimakon saya daga matatar, abin da ya kara ta’azzara lamarin.