
Sarki Muhammad Sunusi II gudanar da Hawan Nasarawa tare da kai ziyarar gaisuwar Sallah ga gwamnan Kano Abba Kabir Yusif, kamar yadda aka saba yi duk Sallah.
Sai dai a wannan lokaci mai karon Sarki da tawagarsa sun kasance a cikin motoci, sabanin yadda aka saba yin hawan a dawakai.
Haka kuma Sarkin ya sauya hanyoyin da ya saba bi, inda bayan ya fito daga gidansa dake kofar Kudu da misalin karfe 9 na safe, ya biyo ta Kofar Nassarawa zuwa kan titin gidan gwamnati, daga nan sai aka yanke aka bi ta Iyaka Road zuwa Sokoto Road zuwa titin zuwa gidan gwamnati.
Sarki Muhammad Sunusi ya samu tarba daga mataimakin gwamna Aminu Abdussalam Gwarzo tare da wasu daga cikin mukaraban gwamnati, inda aka gudanar da jawabai tare da taya juna murnar Barka da Sallah.
