
Gwamnatin jihar Ogun ta ce tattalin arzikinta ya daga cikin shekaru shida daga naira tiriliyan 3 da biliyan dari biyar a 2019 zuwa naira tiriliyan 16 a 2025, duk da kamfanin MAG Group sun zuba jarin fiye da dala biliyan 2.
Gwamnan jihar Prince Dapo Abiodun ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Twitter.
Jawabin nasa na zuwa ne yayin ganwa da wakilan kamfanin MAG Group da suka kai masa ziyara a ofishinsa.
Ya ce an samu wannan nasara ce sakamakon kokarin inganta aikace-aikace da samar da kayan more rayuwa da da kuma kawata dutsen Olumo dake kawowa jihar kudin shiga kimanin naira miliyan 20 duk mako.
Prince Dapo Abiodun, ya bayyana jin dadinsa bisa yadda al’umma ke tururuwar kai ziyara dutsen na Olumo.