Babban Sakataren gwamnatin kasar Al Aminou Lo ne ya bayyana hakan wanda kuma ya janyo ce-ce-kuce tsakanin ma’aikatan kasar.
La’akar da yadda matakin zai kara ta’azzara halin matsin rayuwa da ake ciki da tsadar kayayyaki.
“Domin daidaita al’amuran ƙasar da manufofin da gwamnatin Senegal ta ke son cimma nan da shekarar 2050, za a aiwatar da sauye-sauye saboda rayuwar ƴan ƙasar ta dawo yadda ya kamata.
Wasu lokutan mutane na ƙorafi kan albashi mai yawa a wasu hukumomi” in ji Babban Sakataren kasar
Al Aminou ya kuma kara da cewa, akwai buƙatar masu albashi mai yawa su yi wani ƙokari, ko na wucin-gadi ko kuma na dindindin domin rage albashinsu.
Sai dai a duk wannan yunkuri ba zai taɓa masu ƙananan albashi ba, saboda hakan ba zai yiwu ba, inji shi.
