Jam’iyyar APC na kan gaba a sakamakon zaben kujerun ‘yan majalisun dokokin jiha a kananan hukumomin Kano Municipal da kuma Ungogo.
An gudanar da zaben ne a ranar Asabara da aka yi a jiya Asabar
Rahotanni sun ce Ɗan takarar jam’iyyar APC, Nabil Sarki Aliyu Daneji a karamar hukumar birni shine a gaba da ƙuri’u 7,484
Yayin da Ɗan takarar Jam’iyyar APC, Sa’ad Aminu Sa’ad a karamar hukumar Ungogo ya samu kuri’u 8,975.
Jam’iyyun NNPP da PDP da ADC da ake wa kallon manyan abokan hamayya ba su shiga zaben ba, yayin da NNPP ta ce, ‘yan takarar da APC ta tsayar yayanta ne a don haka bata da wani ja.
Zuwa karfe 3 na daren jiya, an dora kusan kashi 70 na sakamakon zaben karamar hukumar birni a shafin yanar gizo na hukumar zabe ta kasa Irev.
Yayin da aka dora kusan kashi 58 na sakamakon zaben karamar hukumar Ungogo a shafin na Irev.
Tuni dai Jam’iyyar NNPP ta yaba wa Hukumar INEC kan yadda aka gudanar da zaɓen cikin lumana.
wannan na kunshe cikin sanarwar da Sakataren Yaɗa Labaran NNPP a Jihar Kano, Injiniya Ibrahim Karaye, ya fitar a jiya Asabar 21 Fabrairu 2026.
Sanarwar ta ce jam’iyyar ta gamsu da yadda aka gudanar da zaɓen, tare da taya murna ga ’yan takara biyu da ta fara tsayarwa wadanda kuma su ne suka yi nasara.
