Aminu Abdullahi Ibrahim
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bai wa daliban Cyprus 84 aiki nan take.
Daliban sun kammala karatu shekaru da dama da suka gabata, sai dai ba su samu shaidar kammalawa (Certificate) ba saboda rashin biyan kudaden karatunsu da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi.
An tura daliban karatu ne karkashin shirin tallafin karatu na kasashen ketare na Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, sai dai bayan zuwan gwamnatin Ganduje sai ta dena daukar nauyin karatun.
Sai dai gwamna Abba Kabir Yusuf, ya biya bashin da jami’ar Near East Cyprus ke bi na naira biliyan 2,240,000 tare da baiwa daliban shaidar kammala karatun su.
Daliban sun hada da masu digiri na daya da na biyu da suka karanci bangarori daban-daban da suka shafi lafiya da
Da yake jawabi gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bukaci daliban da su hidimtawa al’ummar jihar nan.
Ya ce gwamnatinsa zata cigaba da inganta Ilimi a fadin jihar Kano.
A nasa jawabin matemakin gwamnan Kano Kwamaret Aminu Abdulsalam ya ce duk da daliban sun kammala karatu sun samu sakamako mai kyau amma haka gwamnatin baya tayi biris wajen biyan kudin da za a basu sakamakon su tsohon shekaru.
Ya ce gwamna da kansa ya je har kasar ya zauna da shugabaninta suka amince har ta kai ga gwamnati ta biya kudaden.
Ya ce akwai wasu karin daliban daga wasu makarantun da suma gwamnan Kano ya biya musu kudin makaranta don karɓar sakamakon su.
Ya ce kwannan dalibai zagaye na biyu zasu tashi zuwa kasashe daban daban domin zurfafa karatunsu yana mai cewa kari ne akan na farko guda dubu daya da dari daya.
Ya ce a yanzu babu wata makaranta sabuwa ko tsohuwa da ba a sahale mata yin kwa-kwasai ba a jihar Kano.
Kwamaret Aminu Abdulsalam ya ce suna biyan alawus da kudaden malamai na dukan makarantun gaba da sakandire.
Ya ce duk wani abu da ba a yi ba a bangaren ilimi to baije gaban gwamna ba Amma Indai yaje gabansa to za a ayi.
Taron rabawa daliban shaidar karatun ya samu halarta manyan mutane da sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu.
