Jam’iyyar adawa ta ADC ta buƙaci a cire shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, Farfesa Joash Amupitan.
ADC ta ce hukumar ta koma ƴan amshin shatar jam’iyya mai mulki ta APC, kuma ba za ta iya amincewa da hukumar a zaɓen 2027.
A ranar Laraba ne dai INEC ta cire sunan Sanata David Mark a matsayin shugaban jam’iyyar ADC da Abdulra’uf Aregbesola a matsayin babban sakatare daga shafinta.
INEC ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon hukuncin kotun ƙoli da kuma shari’ar da ke gaban babbar kotun tarayya Abuja dangane da rikicin da ake yi tsakanin ɓangarori biyu wato David Mark da na Nafi’u Gombe.
Sai dai a wani taron manema labarai ƙarkashin jagorancin Sanata David Mark, jagororin ADCn sun ce hankalin jam’iyyar bai kwanta ba da shugabancin INEC.
ADCn ta yi watsi da matakin da INEC ta ɗauka inda ta ce za ta ci gaba da gudanar da harokokinta.
