
Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya (NBS) ta bayyana cewa farashin kaya ya ragu a watan Fabrairun 2025, inda ya sauka zuwa kashi 23.18% bisa dari.
Hukumar NBS ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Litinin, bayan tattara alkalumman hauhawar farashin kayayyaki a watan da ya gabata.
A farkon shekarar 2025, hauhawar farashin kaya ya kai 31.7%, amma an samu raguwar kashi 8.52% daga wannan adadi.
A shekarar 2024, Najeriya ta fuskanci hauhawar farashi mafi muni cikin shekaru 28 bayan da Shugaba Bola Tinubu ya janye tallafin mai tare da sassauta darajar naira.

A watan Fabarairu Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ƙayyade kuɗin ruwa a kashi 27.5%, yana mai cewa hakan na da nufin rage tashin farashi.
Hukumar NBS na ci gaba da bibiyar yanayin tattalin arziki tare da fitar da alkalumma kan hauhawar farashi, wanda ke da matukar tasiri ga rayuwar ‘yan kasa.