
Shugaban Bankin Raya Yankin Afirka (ADA), Mista Akinwumi Adesina ya bayyana cewa matasan Afirka na buƙatar tallafi na jari domin inganta harkokin kasuwancinsu ba kyautar Naira 10,000 ko 50,000 ba.
Adesina ya ce, matasan Najeriya da sauran kasashen Afirka 51 ba sa bukatar tallafin kuɗaɗen kashewa, sai dai taimakon da zai basu damar bunkasa kasuwancinsu da samun arziki.
Shugaban Bankin wanda ya taba rike mukamin Ministan Noma a Najeriya, Ya jaddada cewa akwai matasa sama da miliyan 465 masu shekaru tsakanin 15 zuwa 35 a nahiyar Afirka da ke bukatar tallafin jari da zai su tsaya da kafafunsu.
A cikin wannan mahanga, Adesina ya yi gargaɗin cewa shugabannin yankin ya kamata su mayar da yawan matasan a matsayin kadara, ba tare da yin sakaci ba, domin matasan kada su zama wata baraza ga al’umma.