Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya gabatar da 1 trillion 368 billion a matsayin kasafin kudin jihar na shekarar 2026.
Abba Kabir Yusuf ya gabatar da kasafin kudin ne a gaban Majalisar Dokokin jihar a ranar Laraba.
“Mun cimma nasarar sauke nauyin kashi 80 cikin dari na alkawuran da muka dauka lokacin yakin neman zabe” in ji gwamna a cikin jawabinsa a majalisar.
Kadan daga abin da kasafin kudin ya kunsa:
Bangaren ilimi naira Biliyan N405,350,318,751.17 (30%), yayin da ayyukan raya kasa (Infrastructure) naira Biliyan N346,286,262,957.87 watau kashi (25%)
Bangaren Lafiya N212,250,500,044.11 (16%)
An warewa manyan aiyuka naira 934,640,032,101.00 (Kudin da gwamnati ke kashewa wajen manyan ayyuka da za su daɗe suna amfani, kamar gina tituna, asibitoci, makarantu, sayen manyan kayan aiki, da sauransu.)
Sai kudin gudanarwa N433,487,897,170.00, watau Kudin da ake kashewa akai-akai domin gudanar da aiki na yau da kullum, kamar albashi, biyan wutar lantarki, kayan aiki na ofis, kula da gine-gine, da sauransu.
Za mu kawo muku cikakakkun bayani nan gaba.
