Shugaba Trump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya, a bisa zargin gwamnatin kasar da kyalewa ana yiwa kiristoci kisan Kiristoci.
Hakan na kunshe a wani saƙo da shugaban na Amurka ya wallafa a shafinsa na sada zumunta a ranar Asabar.
“Washington na iya shiga Najeriya da ƙarfin soji don kakkaɓe ƴanta’adda masu kishin Islama da ke aikata ta’asa.
“Na ba ma’aikatar tsaron Amurka umarnin ta fara shirin ɗaukar mataki kan Najeriya idan har gwamnatin Najeriya ta bari ana ci gaba da kashe Kirista,” in ji shi.
Tun a ranar Juma’a Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa ana kashe dubban kiristoci a Najeriya kuma masu tsattsauran ra’ayin Islama ne ke da alhakin kisan, ba tare da ya bayar da wata hujja ba.
Tuni Najeriya ta yi watsi da ikirarin cewa ana kashe kiristoci ba gaira ba dalili a yankin arewacin inda galibi musulmi suka fi yawa.
Najeriya dai ta tade tana fama da tashe-tashen hankula da dama wadanda masana suka ce ana kashe Kiristoci da Musulmai ne ba tare da bambancewa ba.
