Ma’aikatar yada labarai ta jihar Kano tayi kira ga sabbin shugabannin kungiyar tsaffin yan jarida ta jihar Kano, da su jajirce wajen cigaban kungiyar.
Kwamishinan yada labarai Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bukaci hakan yayin wani taro na kaddamar kungiyar.
Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya yace tun a watannin baya ne gwamnati ta kafa kwamitin kwararrun tsofaffin yan jarida, domin samar da sabon daftarin tsari da zai tabbatar da cewa aikin jarida na gudana cikin kwarewa da tsari.
Ya kara da cewa an zabi shugabannin da zasu jagoranci tafiyar kwamitin na tsawon shekara guda.
Wani cikin mahalarta taron kwamitin ya bukaci shugannin kwamitin su yi aiki tukuru domin samun gyara akan aikin da aka dora musu.
Wakilinmu Sufyan Halilu Getso da ya halarci taron ya ruwaito cewa Shugaban kwamitin Mallam Ahmed Aminu ya ce za su yi kokarin aiki bisa doka da ka’ida ta aikin jarida.
