Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umurci dukkan sarakunan jihar da su ci gaba da gudanar da bikin hawan sallah a duk shekara domin raya al’adun gargajiya na jihar Kano.
Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne a lokacin bude bikin Kalankuwa na shekarar 2025, wani taron al’adu na kwana uku da aka shirya domin nuna al’adun Kano da karfafa matasa da masu kere-kere da kuma gina dangantaka ta kasa da kasa.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar yau Asabar, Gwamna Abba ya tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafawa masarautu domin tabbatar da cewa wannan tsohuwar al’ada ta hawan sallah.
A nasa jawabin, Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yaba da kokarin gwamnatin Kano wajen dawo da tsofaffin dabi’u da al’adun mutanen Kano, tare da tabbatar da cewa masarautu za su ci gaba da goyon bayan wannan yunkuri.
Taron ya kunshi nunin al’adu, girke-girke na gargajiya, wasanni, wasan kwaikwayo, sana’o’in hannu da kuma gabatar da makaloli daga masana.
