Wani Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima ya zargi gwamnatin Shugaba Tinubu da rashin aniyyar gudanar da sahihi kuma ingantaccen zaɓe a 2027.
Galadima ya bayyana hakan ne ranar Talata a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise.
Dattijon dan siyasan ya kuma ce, gwamnatin da jam’iyyar APC ke jagoranta ta kankane cibiyoyin gwamnati tare da tafiyar da su yadda take so.
Buba Galadima ya kuma ja hankalin jama’a kan shirin da gwamnatin tarayya ta ke yi na nada wani da ya kira mai lam’a a matsayin sabon shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), yana mai cewa hakan na iya jefa ƙasar cikin wani hali,
Dangane da batun fara yaƙin neman zaɓe da wuri da wasu jam’iyyu ke yi, Buba Galadima ya zargi INEC da gazawa wajen aiwatar da tanade-tanaden dokokin zaɓe.
