
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Myanmar, Janar Min Aung Hlaing, ya isa Thailand domin halartar taron tattalin arziki, kwanaki kaɗan bayan mummunar girgizar ƙasa ta faru a kasarsa.
Masu suka a Myanmar da ƙasashen waje sun ce yakamata a bar shi a gida domin sanya ido kan ayyukan agaji.
Suna ganin gayyatarsa na zuwa Thailand wani ɓangare ne na halasta juyin mulkin sojan da ya faru a ƙasarsa.
A farkon makon nan, wata ƙungiyar ma’aikata ƴan ci-rani a Bangkok ta miƙa koke ga Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ta bukaci a hana Janar ɗin zuwa Thailand.
Ana tsammanin zai iya neman ƙarin taimako domin tunkarar bala’in girgizar ƙasa.