
Kungiyar Ma’ikatan Kananan Hukumomi na Najeriya ta bukaci Gwamnonin jihohi 20 a Najeriya da lallai su soma aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 da gwamnatin tarayya ta kayyade a kasa baki daya.
Shugaban NULGE na ƙasa, Alhaji Haruna Ƙanƙara ya bayyana cewa jihohi kamar Yobe da Gombe da Zamfara da Kaduna da Imo da Ebonyi da Cross River da FCT (Babban Birnin Tarayya) na daga cikin waɗanda har yanzu ba su fara biyan albashin ba.
“Wasu jihohi sun aiwatar da tsarin ga ma’aikatan jiharsu kawai, suna watsi da ma’aikatan ƙananan hukumomi”. In ji shi.
A hirar wakiliyar mu da tsohon sakataren kungiyar Kwadago ta TUC a Kano, kwamared Sani Babangida Idris, ya jaddada cewa rashin aiwatar da sabon albashi na saba wa doka, kuma hakan na iya jawo matakin ladabtarwa daga hukumomi.
A yayin da tattaunawa da gwamnatocin jihohi ke ci gaba, ƙungiyoyin ma’aikata sun jaddada cewa ba za su sassauta ba wajen ganin an yi wa malamai da ma’aikatan ƙananan hukumomi adalci da tabbatar da aiwatar da sabon albashin cikin gaggawa.