Gwamnatin jihar Katsina da Asusun Kula da ƙananan Yara Na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) sun ƙaddamar da shirin inganta harkar rigakafi don kawar da cutar shan inna a jihar.
Hajiya Zulaihat Dikko Radda ce ta ƙaddamar babban birnin jihar a ranar…
Wanda hakan zai sai sa iyaye maza su bada gudummawar su a wajen gudanar da yin rigakafi na yau da kullum a jihar. Inji ta.
Sannnan ta shawarci masu ruwa da tsaki da su rungumi shirin na UNICEF domin kare yara daga kamuwa da cututtukan da za a iya rigakafin su a faɗin jihar.
Ta kuma yi tsokaci kan isar allurar inda ake bukata
ƙarancin allurar rigakafi da rashin fahimtar illar rashin yin allurar rigakafin na cutar shan inna a tsakanin mazauna karkara, na barazana ga rayuwar yara da dama tsawon shekaru.
Da take jawabi yayin ƙaddamar da shirin, babbar jami’ar ofishin UNICEF ta Kano, Mista Rahama Farah, ta ce shirin ya ta’allaka ne na ganin an tabbatar da kawo ƙarshen cutar shan inna a jihar.
