Gwamnatin Jihar Jigawa ta sanar da shirin soma bai wa daliban da suka kammala karatu a makarantun Tsangaya takardun shaidar kammala karatu, da nufin tabbatar da sahihancin karatun da suka yi tare da inganta tsarin ilimin Alƙur’ani a fadin jihar.
Gwamna Jihar, Malam Umar Namadi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan ilimin makarantun Tsangaya, wanda aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Jigawa.
A cewar gwamnan, gwamnatinsa ta riga ta samar da muhimman kayayyakin aiki a makarantun Tsangaya na zamani guda uku da ta gina, a wani ɓangare na ƙoƙarin inganta koyarwa da walwalar dalibai.
Gwamna Namadi ya ƙara da cewa gwamnati na shirin ware wani kaso na musamman a cikin kasafin kuɗin jihar domin tallafa wa harkokin ilimin Alƙur’ani, inda ya jaddada buƙatar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu ruwa da tsaki domin cimma manufofin da aka sa a gaba.
Taron ya samu halartar Mataimakin Gwamnan Jihar Jigawa, Injiniya Aminu Usman, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatum, Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim, da sauran manyan masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da addini.
A ƙarshen taron, an naɗa Gwamna Umar Namadi a matsayin Uban Ƙungiyar Mahaddatan Alƙur’ani ta Ƙasa.
