Gwamnatin jihar Kano ta sanar da haramta amfani da injin sare itatuwa ba tare da izini ba.
Gwamnatin ta kuma kaddamar da sabon tsarin lasisin amfani da injin da ta kira Chainsaw Usage Permit Framework (CUPF) domin dakile sare itatuwa ba bisa ka’ida ba da kuma kare muhalli.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na jihar, Dr. Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Kano ranar Talata.
Haka kuma, duk wanda ya sare bishiya dole ne ya dasa akalla sabbin bishiyoyi biyu a madadin ta.
Dakta Hashim ya kara da cewa, duk wanda ya karya dokar za a ci shi tarar Naira 500,000 tare da kwace injin sa, yayin da wanda ya sare bishiya ba tare da lasisi ba zai biya Naira 250,000 a kan kowacce bishiya, sannan a tilasta masa sake dasa sabbin bishiyu.
Gwamnatin Kano ta ce jami’an tsaro, hukumomin kananan hukumomi, sarakunan gargajiya da kuma masu sa ido daga cikin al’umma za su kasance cikin masu aiwatar da wannan doka.
Kwamishinan ya jaddada cewa yin rijista da samun izini wajibi ne ga duk mai aikin sare bishiya, domin tabbatar da kare albarkatun kasa da kare muhalli.
