Aminu Abdullahi Ibrahim
Kungiyar bin diddigin kasafin kudi da aka warewa fannin lafiya (Africa Health Budget Network) da sauran kungiyoyin bunkasa fannin lafiya sun nuna gamsuwarsu akan gudummawar da gwamnatin Jihar Kano ke baiwa fannin riga kafin yara ta hanyar ƙara kasafin kuɗi a shirin allurar riga-kafi, suna mai cewa hakan alama ce ta jajircewar gwamnati wajen kare lafiyar yara da rage adadin yaran da ba sa samun riga kafi.
Shugaban kungiyar a Kano, Dr. Musa Mohammed Bello, ya bayyana haka a taron bita da inganta hanyoyin aiwatar da shirin riga-kafi wanda aka gudanar anan Kano ranar Laraba.
Ya ce gwamnatin Jihar Kano ta ware fiye da Naira miliyan 350 a 2023 a shirin riga kafi, da Naira miliyan 528 a 2024, sannan ta ƙara zuwa Naira biliyan ɗaya a kasafin 2025, wanda hakan ya nuna kulawar gwamnati wajen ƙarfafa riga-kafi da inganta lafiyar yara.
Sai dai ya buƙaci gwamnati da ta tabbatar ana sakin kuɗaɗen a kan lokaci, domin jinkiri na iya kawo cikas ga aiwatar da shirye-shiryen riga-kafi, musamman ga yaran da ba su taɓa samun allurar ba.
Dr. Musa Mohd Bello ya kuma bayyana ƙalubalen da ake fuskanta wadanda suka haɗa da mummunar fahimtar wasu game da allurar riga kafin da munanan dabi’u daga wasu ma’aikatan lafiya ke nunawa a lokacin riga kafin da kuma rashin isassun cibiyoyin lafiya a wasu yankuna.
A nasa jawabin, Akibu Hamisu na kungiyar Africa Health Budget Network (AHBN) ya ce Jihar Kano na da kaso 15 cikin 100 na yaran ba sa samun riga kafi dalilin da ya sa aka zaɓi kananan hukumomin Sumaila da Kumbotso domin mayar da hankali wajen cike gibin yaran da ba sa samu alluran riga kafin.
Ya yaba wa gwamnatin Kano da shirin tallafawa harkokin lafiya na BHCPF, da kungiyar AFENET, da sauran abokan hulɗa bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen samun ci gaba a shirin riga-kafi.
Shugaban shirin tabbatar da aiwatar da riga kafi ga al’umma wato (CoP), Salisu Yusuf, ya ce taron ya ba da dama wajen ganin dukkan masu ruwa da tsaki a fannin rigakafi a samu a yi bibiya Akan kasafin kudin ma alluran rigakafi irin nasarori da kalubalen da aka fuskanta a shekaru biyu da su Ka wuce.
Sannan da tattauna Akan managartar Ayyukan da hanyoyin da za a bi wajen Samar da ingantaciyar lafiya GA Mata da kananan Yara a shekara mai gabatowa.
