Hukumar Gano Man Fetur ta Kasa ta ce Nijeriya ta yi asarar naira biliyan 118.864 a cikin watanni biyu na farko na 2025, sakamakon gurbacewar iskar gas.
Wannan na zuwa ne yayin da Ministan Kasafin Kudi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Bagudu ya ce gwamnatin tarayya tana amfani da dabarun gida don cimma burinta na sauya makamashi.
A cikin rahoton da ta yi na Janairu da Fabrairu 2025, NOSDRA ta bayyana cewa naira biliyan 118 da aka rasa a cikin watanni biyu na farko na shekara yana wakiltar kashi 31.48 na jimillar adadin da aka rasa sakamakon gurbacewar iskar gas a cikin lokacin.
A cewar hukumar, kamfanonin mai da iskar gas da ke aiki a kasar sun samar da iskar gas na naira biliyan 22.3 daga ayyukansu na teku.
Hukumar ta lissafa asarar ta amfani da Babban Bankin Nijeriya (CBN) na musayar canji na naira 1,520 zuwa dala daya.
