Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan, bai taba gaya masa cewa yana da niyyar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba.
Wike ya fadi haka ne yayin ganawarsa da ’yan jarida a Abuja a ranar Juma’a,
Tsohon gwamnan Jihar Ribas ya kuma ce bai taba samun kiran Jonathan da ya nemi shawara ko goyon baya kan takara ba.
“Ba zan gaskata jita-jitar da ke yawo a jaridu ba, yana mai cewa “ba duk abin da ake rubutawa gaskiya ba ne.”
A game da batun tsohon minista Kabiru Tanimu Turaki (SAN) da ake cewa ya zama dan takarar na masalaha na shugabancin jam’iyyar PDP, Wike ya nesanta kansa da lamarin, yana mai cewa “ba a PDP din da na sani ba ce.”
Ya kuma bayyana cewa ba zai halarci gangamin jam’iyyar da aka shirya a watan Nuwamba ba, saboda a cewarsa “taron ba bisa doka ba ne.”
A gefe guda, ana ci gaba da rade-radin cewa Jonathan na fuskantar matsin lamba daga wasu mutane, ciki har da daga mahaifarsa yankin Naija Delta, da ke son ya janye tunanin takara ya kuma goyi bayan Shugaba Bola Tinubu a wa’adin sa na biyu.
