Kungiyar manoman masara ta kasa ta yi kira ga ‘ya’yan kungiyar da su gaggauta bude asusun ajiya a bankin manoma.
Shugaban kungiyar na kasa, Dakta Bello Abubukar Funtuwa ne yayi wannan kiran a wani taron gaggawa da kungiyar ta kira domin jan hankalin manoman kan muhimmancin bude asusun banki.
Dakta Bello Funtuwa ya kuma ja hankalin mambobin kungiyar da su yi taka-tsan-tsan kan wasu batagari da ke yawo da sunan ‘yan kungiyar suna cutar manoma wajen karbar kudin manoman da sunan bude musu asusun banki, ko kuma rijista ba tare da wata kwakwkwarar shaida ba.
Manoma sun koka da faduwar Farashin abinci a Kasuwa
Batagari sun yiwa yaro dan shekara biyar yankan rago a karamar hukumar Rimin Gado ta jihar Kano
“Duk da karancin sani ga wasu daga cikin manoma a harkar, muna jan hankalin shugabannin manoman jihohi da su shiga lungu da sako domin wayar da kan manoma kan muhimmancin yin rijista da kuma bude asusun bankin.” In ji shi.
Dakta Bello ya kuma ce, an dauki masana a fannin na’ura mai kwakwalwa domin taimakawa manoman karkara domin yin rijistar da kuma bude asusun bankin cikin sauki.
