
Matafiya dake amfani da jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun nuna farin cikinsu da dawowar zirga-zirgan jirgin, sai dai sun koka kan wasu sauye-sauye da suka fuskanta
Jiirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya soma aiki a ranar Laraba,
Matafiya na kokawa kan yadda aka sauya lokutan zirga-zirga da kuma yadda jirgin ke kwashe tsawon awanni 4 kafin ya isa tashar da ya taso, sabanin awanni 2 da ake yi daga Abuja zuwa Kaduna.
A ranar Laraba 1 ga wata oktoba ne jirgin kasan ya dawo aiki tun bayan hatsarin da ya afku a ranar 26 ga watan Agusta, inda mutane da dama suka jikkata.
Layin dogo na jirgin daga Abuja zuwa Kaduna ya kasance daya daga cikin manyan hanyoyin jirgin kasa a kasar nan, wanda a yanzu mafi yawancin matafiya suka fi amfani dashi madadin hanyar mota da aka fi fuskantar matsalar rashin tsaro.