
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan kisan fararen hula da ake yi a wasu jihohin Najeriya, yana mai cewa lokaci ya yi da a kawo ƙarshen hakan.
Shugaban ya fadi hakan ne a ganawarsa da manyan hafsoshin tsaro, a inda Shugaban ya umarci sauya dabarun tsaro da ɗaukar matakan gaggawa don shawo kan matsalar tsaro a jihohin Pilato, Binuwa e da Borno.
A wata sanarwar da Mai Magana Da Yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanugaya wallafa a shafin X, ta bayyana cewa shugaban ƙasar ya nuna bacin ransa bisa yawaitar hare-hare a sassan arewacin Najeriya.
“kashe-kashen da ake yi sun isa haka. Ya zama dole a dakatar da wannan ta’asa da gaggawa.”