Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, da Shehun Borno, Alhaji Abubakar El-Kanemi, sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta gyarawa tare da fadada madatsar ruwa ta Alo domin hana sake afkuwar mummunar ambaliyar ruwa a bana, biyo bayan wadda aka samu a shekarar 2024.
Gwamnan da shehun Bornon Sun yi wannan roko ne a a karshen mako yayin gaisuwar sallah da Shehun kaiwa gwamnan a gidan gwamnati da ke Maiduguri, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa ya ruwaito.
Zulum ya nuna damuwarsa kan yadda aikin dam din ke tafiyar hawainiya, adon haka ya ja hankalin mahukunta kan mayar da hankali kafin kankamar damuna su kammala gyaran, domin gujewa me kaje ya zo.
Gwamnan ya kara da cewa an kafa wani kwamiti a matakin jiha domin samar da dauki cikin gaggawa yayin da ake jiran matakin gwamnatin tarayya.
A farkon wannan shekarar, gwamnatin tarayya ta amince da Naira biliyan 80 don sake gina madatsar ruwan da kuma fadada shi, sakamakon ballewar da ya yi, wanda ya haifar da ambaliyar ruwa a Maiduguri da kewaye.
