
Aminu Abdullahi Ibrahim
Tsohon dan takarar gwamnan Kano a jam’iya PRP ya ce Shugaba Bola Tinubu na tunanin zai iya mayar da Kano jiha mai jam’iyya daya, ba ta hanyar ayyukan cigaba da inganta rayuwar al’umma ba, sai ta hanyar dabarun siyasa” Salihu Tanko Yakasai
Ya bayyana haka ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Laraba.
Ya ce wannan fahimta ta shugaban kasa kuskure ce akan siyasar Kano.
Ya kara da cewa tun daga zamanin NEPU har zuwa lokacin Santsi da Tabo, Kano ba ta taba zama jiha mai jam’iyya daya ba, kuma ba za ta taba zama haka ba.
A cewarsa jihar Kano ba Lagos ba ce.
Ya kara da cewa Kano jiha ce ta siyasar kishin al’umma da tsayawa kan gaskiya, da tarbiyar da Mallam Aminu Kano.
Ya ce suna adawa ne domin neman ci gaban kasa da al’umma, ingantaccen shugabanci, adalci da rikon amana.
Salihu Tanko Yakasai ya ce aka yi wa Kano da zai sa Tinubu yayi tunanin kowa sai ya goyi bayan sa.
Yayi zargin cewa an mayar da hankali kan ayyuka a Lagos da karkatar da nade-nade ga yarbawa kadai yayin da aka yi watsi da korafe-korafen alummar Kano.
A cewarsa biyayya ga shugabanci na samuwa ne ta hanyar adalci da kyautatawa, ba a tilasta shi ta dabarun siyasa da wayo ko cin amana ba.
Idan za a iya tunawa a kwanakin baya ne Salihu Tanko Yakasai ya sanar da komawarsa jam’iyar ADC.
