
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da kyautar fili da kuma naira miliyan biyar (₦5,000,000) ga kowanne gida daga cikin iyalan ’yan tawagar wasanni 22 da suka rasa rayukansu a wani mummunan haɗarin mota da ya auku a watan Yuni 2025.
Mai ba Gwamnan shawara kan harkokin yada labarai, Malam Ibrahim Adam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.
Kyautar, in ji shi, na da nufin rage raɗaɗin rashin da iyalan suka tsinci kansu a ciki, da kuma girmama sadaukarwar waɗanda suka mutu a yayin aikin gina sunan Kano da Najeriya a fagen wasanni.
Tawagar, wadda ta haɗa da ’yan wasa, masu horaswa, jami’an lafiya, direbobi, injiniyoyi da ɗan jarida, sun gamu da ajalinsu ne a hanyar dawowa daga gasar National Sports Festival da aka gudanar a jihar Ogun.
Wannan hatsari ya girgiza al’ummar Kano da ma kasa baki ɗaya, duba da irin nasarorin da tawagar ta samu kafin rasuwar ta.
A cikin gasar da aka kammala, tawagar Kano ta lashe lambar zinare guda shida (6), azurfa goma sha uku (13), da kuma tagulla goma (10) gagarumar nasara da ke nuni da jajircewar ‘yan wasan da ma dukkan masu ruwa da tsaki a fagen horar da su.