
Tsofaffin sojojin Najeriya da suka kwashe kusan mako guda suna zanga-zanga a gaban Ma’aikatar Kuɗi da ke birnin tarayya Abuja, sun dakatar da zanga-zangar bayan samun tabbacin cewa gwamnati za ta biya su hakkokinsu nan da mako daya.
Jagoran zanga-zangar, Ekundayo Alisame, ne ya bayyana haka ga manema labarai, inda ya ce gwamnatin tarayya ta sha alwashin biyan su abubuwan da suke bin ta nan da kankanin lokaci.
Alisame, ya ce daga cikin bukatun tsofaffin sojojin har da biyan su alawus-alawus da gwamnati ke bin su, sauya shugabancin hukumar kula da yan fansho ta soja da kuma inganta walwalar ma’aikatan da suka yi ritaya daga rundunar soja.
Rahotanni sun ce tsofaffin sojojin sun yanke shawarar janye zanga-zangar ne bayan wata ganawa da suka yi da jami’an ma’aikatar kuɗi, hukumar fanshon soji da kuma hukumar walwalar sojoji a wani taro a Abuja.
Tsofaffin dakarun dai sun shafe kusan kwana bakwai suna zanga-zanga saboda a cewarsu, gwamnati na ci gaba da yin burus da yarjejeniyar da aka cimma tun da fari dangane da biyan su hakkokinsu.