
Daga Khalil Yaro
‘yan kasuwar singa sun danganta tsadar kayayyakin masarufi da da ake fama ga masu shago da kanti a unguwanni.
Mai Magana da yawun kungiyar ‘yan kasuwar Singa Rabi’u Usman ne ya bayyana haka a hirarsu da wakilinmu an ranar Asabar.
Kakakin kungiyar ya amsa cewa, farashin kayan abinci ya sauka sosai a kasuwa amma masu sayarwa a shaguna a cikin unguwanni ne suka ki saukar da farashi
“A baya farashin fulawa ya kama daga 70,000 zuwa 80,000 amma yanzu ana sayar da ita a kasuwar singa daga Naira 55,000 zuwa 57,000.
“Haka ma farashin sukari da kuma shinkafa na gida da na waje duk sun sauka amma masu shaguna a unguwanni da gidajen biredi da masu gurasa sun ki rage farashi”. In ji shi.
Rabiu Usman ya kuma bukaci gwamnatin Kano da ta kafa kwamiti da jami’an wadanda za su rinka bibiyar shagunan unguwanni da masu buredi da sauran kananan ‘yan kasuwa don ganin al’umma sun samu sauki.
A hirarsa Abdulrahaman Bashir, wani mai shagon sayar da kayayyaki a unguwar Kankarofi ya tabbatar da raguwar farashin kayan abincin a kasuwa sai dai ya bayar da nasu uzurin na kara farashi ungwanni.