Shugaban Amurka Donald Trump ya ce rundunar sojin Amurka ta kai hari mai girma a Tsibirin Kharg na Iran kuma ya yi gargaɗin cewa za a iya kai hari kan wuraren mai na ƙasar idan aka ci gaba da kawo tangarɗar jigilar jiragen ruwa ata Mashigin Hormuz.
Trump ya bayyana a safiyar Asabar a shafinsa na sada zumunta cewa Hukumar Sojan Amurka da ke aiki a Gabas ta Tsakiya da wasu ƙasashen Asiya ta aiwatar da ɗaya daga cikin manyan hare-haren bam a tarihin Gabas ta Tsakiya kuma ta hallaka duk wani wuri na SOJA a wurin da Iran ke taƙama da shi, Tsibirin Kharg.
Trump ya kara da cewa ya zaɓi kin lalata wuraren mai a tsibirin amman idan Iran, ko wani ya yi wani abu da zai katse wucewar jiragen ruwa cikin ‘yanci da aminci ta Mashigin Hormuz, zai sake tunani nan take.
Tsibirin, wanda yake kusan kilomita 30 daga gabar Iran, yana tafiyar da kusan kashi 90 cikin 100 na fitar ɗanyen mai na Iran, bisa ga wata sanarwa ta baya-bayan nan daga JP Morgan.
Hare-haren Iran na ramuwar gayya sun dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa a Mashigin Hormuz, wanda yawanci kashi ɗaya cikin biyar na ɗanyen mai na duniya da iskar gas na LNG ke bi ta tsibirin, kuma hakan ya shafi wuraren mai a wasu kasashen Gulf.
Trump ya ce rundunar sojin ruwa ta Amurka za ta fara yi wa jiragen ruwa na dakon mai rakiya ta Mashigin Hormuz “nan ba da jimawa ba” don dawo da fitar mai, yayin da yake ƙoƙarin magance hauhawar farashin mai a Amurka.
