Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci ƙasashen da ke cikin ƙungiyar Tsaro ta NATO da su dakatar da cinikin mai da Rasha, sannan sun sanya takunkumi ga ƙasar, kafin Amurka itama ta bi sahu da irin na ta takunkuman.
Shugaban na Amurka ya ce ƙasar a shirye ta ke ta sanya gagarumin takunkumi ga Rasha kan yakinta da Ukraine muddun ƙasashen da ke cikin ƙungiyar NATO su ka fara da sanya irin nasu takunkumin da kuma dakatar da sayen man ƙasar.
Har ila yau, Trump ya kuma bukaci mambobin ƙungiyar ƙasashen da ke yankin tekun Atlantika, su yi la’akari da dora harajin kashi 50 zuwa kashi 100 ga ƙasar China, a matsayin hanyar da za ta taimaka wajen kawo ƙarshen yakin Rasha a Ukraine.
Trump ya sha yi wa Rasha barazanar ƙarin takunkumi – ciki har da wanda ya yi mata a ƙarshen makon da ya gabata bayan da Kremlin ta ƙaddamar da hare-hare ta sama mafi girma a kan Ukraine, amma har yanzu ya kasa daukar wani mataki na zahiri, lamarin dake fusata Ukraine.
