Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana fatan ganin cimma zango na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza cikin gaggawa, tare da gargadin cewa Hamas za ta fuskanci matsala mai tsanani idan ba ta ajiye makaman ta ba da wuri.
Trump ya yi wannan bayani ne yayin ganawarsa da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, a Florida a ranar Litinin.
A taron manema labarai bayan ganawar, Trump ya ce Isra’ila na aiwatar da shirinta dari bisa dari, duk da cewa sojojinta har yanzu na ci gaba da kai hare-hare a Gaza.
Trump ya kara da cewa Amurka na iya goyon bayan wani babban hari kan Iran idan kasar ta sake komawa gina shirye-shiryen makaman linzami ko na nukiliya.
A martanin wannan barazana, Ali Shamkhani, babban mai ba da shawara ga jagoran Iran, ya ce duk wani hari kan Iran zai fuskanci amsa mai tsauri nan take.
