Shugaban Amurka Donald Trump ya gana da Firaministan Isra’ila Benyamin Netanyahu a jihar Florida, inda suka tattauna kan halin da ake ciki a Gaza da kuma wasu muhimman batutuwan.
Wannan ita ce ganawa ta shida tsakanin shugabannin biyu tun bayan dawowar Trump fadar White House a farkon shekarar nan, lamarin da ke nuna ci gaba da kusancin alakar siyasa a tsakaninsu.
Rahotannin BBC sun nuna cewa Amurka ta kasance babbar mai tallafawa Isra’ila tun bayan barkewar yakin Gaza kimanin shekaru biyu da suka gabata.
Sai dai wannan ganawa na zuwa ne a wani muhimmin lokaci, a matsayin gwaji ga alakar Amurka da Isra’ila, musamman yayin da Isra’ila ke shirin tunkarar babban zaben kasa da aka shirya gudanarwa a watan gobe.
Da yake zantawa da manema labarai yayin isowar Netanyahu, Trump ya bayyana fatan cewa za a hanzarta cimma matsaya kan kashi na biyu na yarjejeniyar da ke da nufin kawo karshen yakin Gaza.
