
Sule Lamido ya ce, za su ci gaba da yin gwagwarmaya da kuma kokarin hadakan duk wani mai fada-aji a siyasar Najeriya don tabbatar da ci gaban kasar da kuma kare dimukaradiyya.
Tsohon gwaman Jigawa kuma daya daga cikin dattawan babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, fai hakan ne a hirarsa da BBC a ranaar Laraba.
“Na sha fadin cewa idan kana tunkarar abu, to baka kawo rashin nasara a cikinsa.
“Ko shakka babu muna ta fadi tashin ganin mun yi sulhu a inda ya kamata a yi, sannan muna wayoyi da kuma tuntubar juna domin Najeriya ta ci gaba, kuma ba muna yi don kanmu ba ne sai don al’ummar Najeriya. In ji shi.
Alhaji Sule Lamido, ya kuma kara da cewa, a cikin abubuwan da ya ke yi har da kokarin warware rikicin jam’iyyarsu ta PDP.
A baya-bayan nan Sule Lamido, ya gana da wasu manyan ‘yan siyasa a Najeriya, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.